Mun San Inda Masu Satar Mutane Suke, Muna Tsoron Matsala ne Kawai, Lai Muhammed


Ministan yaɗa labarai da al'adu, Alhaji Lai Muhammed, ya tabbatarwa yan Najeriya cewa gwamnati na ƙoƙarin kawo ƙarshen matalar tsaro a ƙasar nan.

Ministan yace zargin da wasu mutane suke cewa gwamnati bata damu da ta magance waÉ—annan matsalolin ba bashi da tushe balle makama.

Ya Æ™ara da cewa ba da jimawa ba yan Najeriya zasu ga sakamakon Æ™oÆ™arin da gwamnati take na dawo da zaman lafiya a Æ™asar nan, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Ministan ya faÉ—i haka ne a wani jawabi da yayi a jihar Lagos, yace:

"Ba wani sabon labari bane cewa Najeriya na fama da matsaloli kala daban-daban na tsaro, na karanta wasu magan-ganu dake cewa gwamnati tana rufa-rufa kuma bata da dabarun yadda zata magance matsalolin."

"Ina mai tabbatar wa yan Najeriya cewa yayin da gwamnati ta fahimci ƙalubalen tsaron da ake fama dashi; ta'addanci, yan bindiga, satar mutane, da rikicin manoma da makiyaya, gwamnati ba ta lulluɓe komai."

"Kuma gwamnati ta tanadi duk abinda yakamata domin kawo ƙarshen matsalar kamar yadda zaku gani bada jimawa ba."

Muhammed ya ƙara da cewa gwamnati tasan maɓoyar masu satar mutane, ya ce hukumomin tsaro na bi a hankali ne saboda gudun haɗawa da fararen hula.

Yace: "Wuraren ɓoyon waɗannan masu satar mutanen ba abune boyayye a wajen jami'an tsaro ba, suna bi a hankali ne tare da kulawa domin gujewa cutar da mutanen da suka je kuɓutarwa."

"Jami'an tsaro suna da duk abinda ake buƙata domin magance ƙalubalen tsaron da Najeriya ke fama dashi."

Source: Legit Newspaper


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/IM8Uuxtia6qBsdKcEszx7s

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN