Sheikh Dahiru Bauchi ya gudanar da sallar Idi a Bauchi


Fitaccen malamin addinin Musuluncin nan na Najeriya, Sheikh Dahiru Usman Bauchi, ya gudanar da sallar Idi tare da dimbin mabiyansa ranar Laraba.

Malamin ya gudanar da sallar Idi ne a gidansa da ke birnin Bauchi a arewa maso gabashin kasar.

Daya daga cikin 'ya'yan malamin, Tijjani Sheikh Dahiru Bauchi, shi ne ya ja sallar ta Idi yayin da malamin yake cikin mamu.

Bayan idar da sallar, Sheikh Dahiru Bauchi ya ce sun gudanar da sallarsu ta Idi ne saboda an tabbatar musu da ganin watan Shawwal ranar Talata.

A cewarsa, "Dangane da wadannan labarai na cewa wata ya tabbata, abin da aka ce adilai guda biyu idan sun gani ya isar mana jama'a, ko kuma jama'a masu yawa [idan sun ga watan]."

Ya kara da cewa an ga wata a wurare irin su Gombe da Gadau da kuma Kebbi.


Shiekh Dahiru Bauchi ya ce ba su da ikon karyata mutanen da suka tabbatar da ganin wata "saboda suna da yawa. Shi ya sa yanzu muka zo muka gudanar da Sallah Idi domin watan Ramadana ya kare, watan Shawwal ya shigo."

Galibin Musulman Najeriya za su gudanar da sallar Idi ce ranar Alhamis bayan Kwamitin da ke bai wa Sarkin Musulmi shawara kan harkokin addini tare da hadin gwiwar Kwamitin Duban Wata a Najeriya sun ce ba su samu rahoton ganin jaririn watan Shawwal a kasar ba ranar Talata 11 ga watan Mayun 2021 wanda ya yi daidai da 29 ga watan Ramadan 1442 AH.

Hakan ne ya sa Sarkin Musulmi, Sultan Muhammad Sa'ad Abubakar, ya ayyana Alhamis 13 ga watan Mayu 2021 a matsayin ranar Sallah kuma 1 ga watan Shawwal.

Rahotun BBC Hausa


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/IM8Uuxtia6qBsdKcEszx7s

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN