Mansurah Isah ta sanar da rabuwar aurensu da Jarumi Sani Danja


A cikin kwanakin da suka gabata ne ake ta rade-radin rabuwar aure tsakanin jarumi Sani Danja da matarsa, tsohuwar jaruma Mansurah Isah.

Hakan ya biyo bayan wata wallafa da tsohuwar jarumar tayi a shafinta na Instagram amma ta goge bayan minti hudu kacal.

Sai dai duk da gogewar da tayi, akwai wadanda suka ga rubutun amma da kyar mujallar fim ta samo wanda ya dauka hoton rubutun saboda rashin dadewar da yayi a shafinta na Instagram din.

Kamar yadda tsohuwar jaruma Mansurah Isah ta wallafa, tace rabuwar aurenta da Jarumi Sani Danja shine mafi a'ala a garesu baki daya.

Idan zamu tuna, jaruman sun yi aure ne a shekarar 2007, auren da koyaushe ake kwatance da shi idan aka ce jaruuman Kannywood basu zaman aure kuma aurensu baya karko.

Allah ya albarkaci auren da 'ya'ya hudu, mace daya, Khadijatul Iman da kuma yara maza hudu masu suna: Khalifa Sani, Yakubu da Yusuf.

An gano cewa ba wannan ne karon farko da Jarumi Sani Danja ya fara sakin matarsa ba, ya taba sakinta a lokacin da suke zama a Abuja, zamanin mulkin tsohon shugaban kasa Jonathan amma sai aka sasantasu.

Mansurah Isah ta sanar da rabuwar aurensu da Jarumi Sani Danja

Mansurah Isah ta sanar da rabuwar aurensu da Jarumi Sani Danja. Hoto daga fimmagazine.com

Kamar yadda Mansurah Isah ta wallafa a shafinta na Instagram: "Muna bada hakuri a kan kunyar da muka baiwa masoyanmu, 'yan uwa da abokan arziki.

"Ni da Sani Danja bamu tare. Bamu son batawa kowa amma wannan rayuwarmu ce kuma hukuncinmu ne.

"Muna son kowa ya mutunta haka saboda mun san ma'anar hakan. Mun damu da juna kuma a koyaushe muna taimakon juna.

"Amma muna tunanin hakan ne yafi dacewa. Akwai bukatar ya cigaba a rayuwarsa nima haka. Mun gode da fahimtarku."

A wani labari na daban, gwamnatin tarayya ta sanar da cewa sabon albashi na musamman na malaman makaranta wanda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince dashi a 2020 zai fara aiki a ranar 1 ga watan Janairun 2022.

Wannan na kunshe ne a wata wallafa da gwamnatin Najeriya tayi a shafinta na Twitter a ranar Laraba 26 ga watan Mayun 2021.

Wani bangare na wallafar yace: "Sabon albashi na musamman na malaman makaranta wanda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince dashi zai fara aiki a ranar 1 ga watan Janairun 2022."

Source: Legit.ng

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/IM8Uuxtia6qBsdKcEszx7s

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN