IBB saurayina ne amma yanzu bama tare domin na rabu da shi, in ji Ummi Zee Zee

Ummi Ibrahim, fitacciyar tsohuwar jarumar Kannywood wacce aka fi sani da Ummi Zee Zee, ta tabbatar da rade-radin da ke cewa ta yi soyayya da Shugaban kasa a mulkin Soja, Ibrahim Babangida (IBB).

Babangida ya mulki Najeriya tsakanin 1985 da 1993.

Akwai rahotanni a shafukan sada zumunta da ke cewa jarumar tana soyayya da tsohon Shugaban Kasar.

A cikin zantawa da Mujallar Daily Trust ta karshen mako, Zee Zee ta ce ta rabu da IBB.

“Tsohon Shugaban kasa Janar Ibrahim Badamasi Babangida saurayina a baya amma ba yanzu ba.

“Duk da haka, a yanzu muna abota kuma muna mutunta juna. A yanzu haka, ina da wani saurayi wanda baya masana’antar nishadantarwa kuma muna shirin yin aure insha Allah. ”

Tsohon shugaban kasar ya rasa Maryam, matarsa a shekarar 2009 kuma bai sake yin aure ba tun lokacin.

Har yanzu kungiyar watsa labarai ta IBB ba ta mayar da martani ba game da ikirarin Zee Zee na yin soyayya da dattijo Shugaban kasar ba.

Source: Legit


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/IM8Uuxtia6qBsdKcEszx7s

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Previous Post Next Post

Information


Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/EsSeIwnS18mKkhQwHP3mFx

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari