Da Ɗumi-Ɗumi: Yan Bindiga Sun Sace Ɗan Majalisa a Jihar Nasarawa


Wasu yan bindiga sun sace ɗan majalisar dokokin jihar Nasarawa, mai wakiltar mazaɓar Nasarawa ta tsakiya, Hon Ismai Danbaba, kamar yadda the nation ta ruwaito.

Rahoton Dailytrust ya bayyaɓa cewa An sace Ɗanbaba ne da yammacin ranar Asabar a kan hanyarsa ta zuwa Jos, jihar Plateau, tare da direbansa da wasu mutum biyu.

Shugaban kwamitin hulɗa da jama'a na majalisar jihar, Hon Mohammed Omadefu, shine ya tabbatar da lamarin ga manema labarai ranar Lahadi.

Yace lamarin ya faru ne a dai-dai dajin ƙaramar hukumar Sanga, dake jihar Kaduna.

Yace ɗan majalisar ya wuce garin Andaha ƙaramar hukumar Akwanga jihar Nasarawa, inda ya nufi Dajin Sanga, a nan ne yan bindigan suka farmake shi kuma suka yi awon gaba dashi.

Omadefu, wanda ke wakiltar mazaɓar Keana a majalisar dokokin Nasarawa, ƙaraƙashin jam'iyyar APC, yace:

"Yan bindigan sun tuntuɓi majalisar dokokin jihar amma har yanzun basu nemi a basu kuɗin fansa ba."

Da aka tuntuɓi kakakin hukumar yan sandan jihar Nasarawa, ASP Ramhman Nansel, Yace lamarin ba'a jihar Nasarawa ya faru ba saboda haka ba zai iya cewa komai ba.

A wani labarin kuma Gwamna Wike Ya Bayyana Matsayarsa Kan Tsayawa Takarar Shugaban Ƙasa a 2023

Gwamnan Rivers, Nyesom Wike , ya bayyana matsayarsa kan tsayawa takarar shugabancin ƙasar nan a zaɓen 2023 dake tafe.

Wike yace idan yana da muradin tsayawa takara a jam'iyyarsa ta PDP, babu wanda ya isa ya dakatar dashi.

Source: Legit Newspaper

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/IM8Uuxtia6qBsdKcEszx7s

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN