Da Ɗumi-Ɗumi: Wasu Yan Bindiga Sun Kashe Tsohon Alƙalin Babbar Kotun Jihar Enugu


Wasu yan bindiga da ba'a san ko su waye ba sun kashe tsohon alƙalin babbar kotun jihar Enugu, Justice Stanley Nnaji, ranar Lahadi da daddare, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Nnaji, wanda ya fito daga ƙaramar hukumar Isi-Uzo, an harbe shi ne a kusa da wata cibiyar binciken cututtuka, lokacin da maharan suka tare shi suka fito dashi daga cikin motarsa.

Da yake tabbatar da kisan, kwamishinan yan sandan jihar Enugu, Mohammed Ndatsu Aliyu, yace ya ƙaddamar da bincike kan maharan da ba'a san ko su waye ba, waɗanda suka yi awon gaba da motar mamacin.

A jawabin da kakakin rundunar yan sandan jihar, Daniel Ndukwe, ya fitar, kwamishinan yace an gaggauta kai alƙalin asibiti, inda likita ya tabbatar da rai yayi halinsa.

Ya kuma ƙara da cewa a yanzun haka an ajiye gawar mamacin a ɗakin ajiye gawa dake asibiti.

Yace: "Ina tabbatar da cewa ba zamu bar wannan lamarin ya wuce hakanan ba, zamu binciko duk masu hannu a kan wannan kisan."

"Ina kira ga mazauna jihar Enugu da su cigaba da bin doka sau da ƙafa, sannan kuma su taimaka wa jami'an yan sanda da bayanai domin ganin an kamo waɗannan yan ta'addan."

A wani labarin kuma Yan Bindiga Sun Kashe Wani Hamshaƙin Ɗan Kasuwa a Ibadan

Wasu yan bindiga sun harbe wani hamshaƙin ɗan kasuwa har Lahira a Ibadan, babban birnin jihar Oyo.

Bayan sun harbi mutumin, maharan sun caka masa wuƙa a ƙirji domin su tabbatar bai tsira da ransa ba.

Source: Legit

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/IM8Uuxtia6qBsdKcEszx7s

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN