Da Ɗumi-Ɗumi: Sarkin Katsina Ya Tunɓuke Rawanin Wani Hakimi Bayan Gano Yana Taimakawa Yan Bindiga


Majalisar sarkin Katsina, Alhaji Abdulmumini Kabir Usman, ta tumɓuke rawanin hakimin ƙanƙara biyo bayan gano cewa yana da hannu dumu-dumu wajen taimaka wa yan bindiga.

Katsina Daily post ta wallafa a shafinta na facebook cewa masarautar ta gano sarkin Pauwan Katsina kuma hakimin ƙanƙara, Alhaji Yusuf Lawal yana taimaka wa wasu yan bindiga wajen gudanar da ayyukan ta'addacin su.

Bisa wannan dalilin ne majalisar sarki ta tsige shi daga muƙaminsa na Sarkin Pauwa hakimin kankara kwata-kwata.

Legit.ng hausa ta gano cewa a kwanakin baya majalisar sarkin ta dakatad da hakimin bisa zarginsa da hannu wajen taimaka wa yan bindigan dake kai hare-hare a faɗin jihar ta Katsina.

A rahoton da katsina daily post ta ruwaito ya nuna cewa sakataren fadar mai martaba sarkin Katsina kuma sarkin yaƙin Katsina, Alhaji Bello Mamman Ifo, shine ya tabbatar da tsige hakimin.

A wani labarin kuma IGP Yayi Magana Kan Barazanar Kai Hari Abuja da Plateau, Yace Mutane Su Kwantar da Hankalinsu

Muƙaddashin sufetan yan sanda na ƙasa, Usman Alƙali Baba, yace babu wani abun tsoro kan barazanar kawo hari Abuja da Plateau.

Kakakin hukumar yan sanda, Mr Frank Mba, shine ya bayyana haka a wani saƙo da ya fitar ranar Juma'a a Abuja.

Source: Legit


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/IM8Uuxtia6qBsdKcEszx7s

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN