An shiga zaman ɗar-ɗar a Ogba, jihar Legas kan zargin harbe wani ɗan acaɓa da wani ɗan sanda ya yi.
Wata majiya ta shaidawa The Punch cewa rikicin ya fara ne tun juya a lokacin da ɗan sandan ya ƙi biyan ɗan acaɓan kudin ɗaukansa da ya yi.
Wata majiya da ta nemi a ɓoye sunanta ta shaidawa majiyar Legit.ng cewa an kashe mutum biyu a daren jiya Alhamis.
"Faɗa ne tsakanin ƴan sanda da ƴan acaɓa. Ɗan acaɓa ya ɗauki ɗan sanda zuwa wani wuri a jiya, sai ya tambayi kuɗin aikinsa daga hannun ɗan sandan bayan ya sauke shi. Ɗan sandan ya ƙi biyan shi kuɗin sannan ya harbe shi.
"An ji ƙarar harbe-harbe a yau da safe. Mintuna ƙalilan da suka shuɗe. Dukkan ƴan acaɓa sun sauka daga baburansu suna shirin yin zanga-zanga," a cewar majiyar.
Ku saurari ƙarin bayani ...
Source: Legit
https://chat.whatsapp.com/IM8Uuxtia6qBsdKcEszx7s
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari