Wani bawan Allah mai suna Gebriel ya Musulunta a babban Masallacin Juma'a na jihar Kebbi Central Mosque ranar Juma'a. Ya karbi sunan Abubakar bayan ya Musulunta.
Shafin labarai na ISYAKU.COM ya samo cewa Abubakar dan asalin kasar Togo ne mazauni garin Birnin kebbi na tsawon shekara biyu, kuma mai sana'ar yin POP na ginin zamani.
Abubakar magidanci ne wanda iyalinsa ke zaune a kasar Togo ya ce:
"Na Musulunta ne saboda na gamsu da yadda Musulmi ke ibadarsu tare da gode wa Allah ta hanyar yin tawakkali da Allah".
"Iyalin mahaifina suna bautar gumaka ne a kasar mu. Ba wata matsala da zan fuskanta saboda na Musulunta, domin babu wanda ya damu da addinin wani a zuri'armu. Duk addinin da ka gan dama za ka yi" Inji Abubakar.
DAGA ISYAKU.COM
https://chat.whatsapp.com/IM8Uuxtia6qBsdKcEszx7s
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari