Jami'an tsaron Najeriya sun shiga shirin ko ta kwana sakamakon rahotannin kashe shugaban Boko Haram Abubakar Shekau.
Da yammacin ranar Laraba, an sami rahotannin da ke nuna cewa an kashe Shekau lokacin da ake gwabza fada tsakanin ISWAP da Boko Haram a dajin Sambisa. Kungiyoyin biyu sun dade basu ga maciji da juna a mazauninau da ke yankin tafkin Chadi.
Sai dai wani rahotun sirri da Jaridar Daily Trust ta sami gani, ya ce wani Kwamandan ISWAP mai suna Baana Duguri ya ce mayakan ISWAP da na Shekau sun gwabza fada ranar Laraba.
Ya ce mayakan ISWAP sun dade suna neman kama Shekau da ransa, amma Shekau ya kashe kansa da kansa bayan ya ta da bam da ke hannnunsa kuma ta tashi da shi ya mutu domin kada a kama shi da ransa.
Har yanzu hukumomin soji basu ce komi ba dangane da zancen kashe Shekau. Sai dai wata babban majiyar tsaro ta gaya wa Jaridar Daily Trust cewa an tabbatar da ikirarin ISWAP na mutuwar Shekau.
Rahotanni sun ce hukumomin soji da na DSS suna aiki kan tantance hakikanin gaskiyar ikirarin ISWAP na kashe Abubakar Shekau shugaban kungiyar Boko Haram.
Abukakar Shekau ya dare ragamar shugabancin kungiyar Boko Haram ne a shekarar 2009 bayan kashe wanda ya kirkiro kuma ya assasa kungiyar Boko Haram Muhammed Yusuf.
https://chat.whatsapp.com/IM8Uuxtia6qBsdKcEszx7s
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari