Hukumar yan sanda a jihar Ogun ta damke wata mata mai suna Olanshile Nasirudeen, kan laifin dabawa mijinta wuka har lahira kan zargin ya yiwa wata mata ciki.
Kakakin hukumar yan sandan jihar, Abimbola Oyeyemi, ya bayyana hakan ga manema labarai, rahoton Premium Times.
Marigayin mai suna, Jimoh Nasirudeen, ya kasance mahauci kuma tare da matarsa yake aikin fawa a Ijebu-Ode.
Kakakin yan sandan ya ce Olanshile ce mata ta hudu a hannun marigayin.
A jawabin da hukumar ta saki, tace: "An damke matar ne bayan kiran da DPO na Obalende dake Ijebu-Ode ya samu cewa matar ta ga wacce mijinta ya yiwa ciki kuma ta fara tuhumarta kan shin ta wani dalili za ta bari mijinta yayi mata ciki."
Hukumar ta kace daga nan aka fara mujadala tsakanin matar da mijinta.
"Kawai sai ta dauki wuka ta bugawa marigayin a bayansa, kuma hakan yayi sanadiyar tsinkewar jijiyarsa. Da wuri aka kaishi asibiti kuma daga baya aka garzaya da shi asibitin General na Ijebu Ode inda ya yi numfashinsa na karshe saboda zubar jini," Kakakin yan sandan ya kara.
Bayan haka matar ta gudu amma aka damke a unguwar Mobalufon da ta boye, cewar yan sanda.
"Yayin bincike, matar wacce take Amaryar ga marigayin ta ce mijinta ne ya fara faska mata maru saboda kawai ta kalubalanci matar da ya yiwa ciki."
A riwayar DailyPost, Mr Oyeyemi ya ce an mikawa iyalan mamacin gawar mutumin domin jana'izarsa bisa addinin Musulunci.
Source: Legit.ng
https://chat.whatsapp.com/IM8Uuxtia6qBsdKcEszx7s
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari