Da duminsa: Ana artabu tsakanin jami'an tsaro da yan bindiga a jihar Imo


Tsagerun yan bindiga da ake zargin matasan IPOS/ESN ne sun shiga artabu da jami'an runduna ta musamman watau 'Special Forces' bayan bankawa ofishin yan sandan Orji, dake Owerri, wuta.

Misalina karfe 12 na rana, yan bindiga sun dira unguwar Orji dake birnin jihar kuma suka bankawa ofishin yan sanda wuta.

Wani mai idon shaida ya bayyanawa Vanguard cewa kawo misalin karfe 12:55 na ranar Talata, sun ga yan bindiga sanye da kaya mai launin baki da ja suna kona ofishin yan sandan.

Wannan abu ya rutsa da iyayen yara da suka je daukan yaransu daga Makaranta.

A riwayar Punch, harsashi ya bugi wata mata sakamakon wannan artabu da yan bindigan keyi da jami'an tsaro.

Matar ta kasance mai sayar da kaya a kusa da inda ake artabun.

Yanzu haka gawarta na kwance a kasa yayinda makwabta ke rusa kuka.

Wannan hari ya biyo bayan harin da wasu tsagerun ya bindiga suka kai Iwolo Oghe, ofishin hukumar yan sanda Najeriya dake Ezeagu, jihar Enugu.

Guardian ta tattaro cewa yan bindigan sun hallaka mutum biyar a mumunan harin da suka kai daren Litinin, 24 ga Mayu, 2021.

Bayan haka yan bindigan sun bankawa ofishin yan sandan wuta.

Source: Legit.ng

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/IM8Uuxtia6qBsdKcEszx7s

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN