Bayan Ƙin Halartar Jana’izar COAS, Shugaba Buhari Yayi Magana da Matar Janar Attahiru a WayaShugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, yayi wa Hajiya Fati ta'aziyya, matar marigayi shugaban rundunar sojin ƙasa, Janar Ibrahim Attahiru, ta wayar salula.

Janar Attahiru tare da wasu manyan jami'an soji sun rasa rayukansu a wani hatsarin jirgi da ya rutsa dasu a jihar Kaduna.

Anyi jana'izarsu sannan aka burne su a maƙabartar rundunar soji dake babban birnin tarayya Abuja.

Wannan na ƙunshe ne a wani jawabi da mai taimaka wa shugaban wajen yaɗa labarai, Bashir Ahmad, ya fitar a shafinsa na kafar sada zumunta tuwita @BashirAhmad.

Shugaba Buhari ya bayyana marigayin a matsayin gwarzon soja wanda yayi yaƙi ba ɗare ba rana ga ƙasar sa Najeriya har ƙarshen rayuwarsa.

Jawabin Bashir Ahmad, yace:

"Da yammacin nan, shugaba Buhari yayi magana da Mrs. Fati Ibrahim Attahiru, matar marigayi shugaban rundunar sojin ƙasa da kuma sauran iyalan jami'an sojin da suka rasa ransu."

"Buhari ya bayyana marigayi COAS Attahiru a matsayin jarumi, gwarzo wanda yayi yaƙi domin Najeriya har zuwa ƙarshen rayuwarsa. Shugaban ya kuma yaba da irin sadaukarwar da jami'am sojin suka yi, waɗan da suka rasa rayuwarsu da kuma jami'an tsaro baki ɗaya."

"Ya ƙara da cewa yan Najeriya zasu cigaba da yaba musu da basu dukkan goyon baya ba tare da tsoro ba, hakan zai ƙara ƙarfafa wa sojojin mu guiwa wajen fuskantar barazanar tsaro da ƙasar mu ke fama da ita."

"Ya tabbatar wa da matan cewa Najeriya ba zata taɓa mantawa da wannan ƙololuwar sadaukarwar da mazajen su suka yi ba. Ya roƙe su da su zuba wa zuciyoyin ruwan sanyi su ɗauki dangana a wannan yanayi mai matuƙar wahala a garesu."

Shugaba Buhari ya umarci ma'aikatar tsaro da hedkwatar tsaro ta ƙasa da su samar da duk wani abu da ya dace ga iyalan mamatan domin rage musu radaɗin wannan babban rashi da suka yi..

Source: Legit

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/IM8Uuxtia6qBsdKcEszx7s

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN