Labari mai zafi: Ana shirin zabe, IPOB sun banka wuta, sun kona ofishin INEC a duhun dare


Hukumar gudanar da zabe na kasa, INEC ta sake gamu wa da cikas a lokacin da ta ke koka wa a kan matsalar tsaro, inda aka kona wani ofishinta.

A cikin daren Litinin, 24 ga watan Mayu, 2021, jaridar Daily Trust ta rahoto cewa, ofishin INEC na jihar Anambra da ke garin Awka ya na ci da wuta.

Rahotanni sun bayyana cewa ana zargin ‘yan kungiyar IPOB masu rajin samar da kasar Biyafara ne suka yi wannan aiki, su ka sa wa ofishin wuta.

Wadannan ‘yan bindiga sun burma cikin babban ofishin INEC mai zaman kanta, suka cinna wuta bayan cin karfin jami’an ‘yan sanda da suke wurin.

Jaridar ta ce ‘yan bindigan na kungiyar Independent People of Biafra sun yi ta faman ba-ta-kashi da ‘yan sanda, aka yi musayar wuta a a daren na jiya.

‘Yan bindiga sun yi wannan danyen aikin ne a lokacin da ake lissafin saura watanni biyar rak INEC ta gudanar da zaben sabon Gwamna a Anambra.

Daga lokacin a IPOB ta fara wannan ta’adi, ta kona ofisoshin hukumomi da gwamnati da-dama.

Jaridar Vanguard ta ce bayan ofishin INEC, ‘yan bindigan su auka wa wani ofishin ‘yan sanda a garin Awka, An kai harin ne da kimanin karfe 8:00 na dare.

‘Yan bindigan sun zo ne a cikin wata mota kirar Hilux, suka shiga buda-wuta a kan titi kafin su isa zuwa ofishin INEC, hakan ya sa mutane duk suka tsere.

Jami’in REC na jihar Anambra, Dr. Nkwachukwu Orji, ya ce ya samu labarin an kawo masu hari, amma bai iya bada wani cikakken bayani ba a cikin daren.

Kafin nan an ji shugaban hukumar INEC ya na kukan cewa an kona ofishinsu 21 a fadin Najeriya, wanda hakan zai iya kawo cikas a zabe mai zuwa na 2023.

A dalilin haka ne hukumar INEC ta shirya wani zama na musamman da shugabannin hafsoshin tsaron Najeriya da duk manyan kwamishinoni zabe na kasa.

Source: Legit.ng

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/IM8Uuxtia6qBsdKcEszx7s

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN