Bankwana: Hayaniya tsakanin iyalan COAS da sojoji ya kawo jinkirin birne shi


An samu karamar hayaniya a ranar Asabar tsakanin iyalan marigayi shugaban sojin kasan Najeriya, Laftanal Janar Ibrahim Attahiru da rundunar sojin Najeriya yayin birne shi.

Wannan rashin jituwan ne ya kawo jinkirin birne shi domin kuwa iyalansa sun jaddada cewa ba za a birne shi da akwatin gawa ba sai dai yadda addinin Musulunci ya tanadar.

Amma wasu manyan hafsoshin soji sun jaddada cewa dole ne a birne gawar Attahiru kamar yadda al'adar soji ta tanadar, The Punch ta ruwaito.

Bayan wani lokaci, manyan sojojin sun shawo kan iyalansa kuma an fadada kabarinsa zuwa yadda zai dauka akwatin gawar.

Attahiru da sauran sojoji 10 sun yi hatsarin jirgin sama ne a ranar Juma'a a filin sauka da tashin jiragen sama dake Kaduna.

An gano cewa jirgin dauke da sojoji mai lambar rijista 5N-R203 zai sauka a sansanin dakarun sojin sama dake Mando Kaduna amma ya koma ya sauka a filin jirgin sama na Kaduna saboda yanayin gari mara kyau.

Baya ga Attahiru, akwai Birgediya Janar Ahmed Kuliya, O Olayinka da MI Abdulkadir, Manjo N Hamza, Manjo LA Hayat, Sajan O Adesina da Umar. Akwai matukan jirgin OM Oyedepo, TO Asaniyi da AA Olufade.

A wani labari na daban, sojoji sun rufe yankin da jirgin dakarun sojin saman Najeriya yayi hatsari a ranar Juma'a a filin suaka da tashin jiragen sama na Kaduna.

Jirgin saman wanda ke dauke da shugaban sojin kasa na Najeriya, Laftanal Janar Ibrahim Attahiru da wasu manyan sojoji ya fadi a filin jirgin inda ya kashe dukkan mutum 11 da ke ciki har da matukan jirgin.

A yayin jawabi kan lamarin, manajan filin jirgin sama na Kaduna, Amina Salami ta sanar da Channels TV cewa hukumar sojin Najeriya sun mamaye yankin da lamarin ya auku.

Source: Legit Newspaper

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/IM8Uuxtia6qBsdKcEszx7s

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN