Da Ɗuminsa: Sarkin Katsina Ya Naɗa Sabon Hakimin Kanƙara bayan tsige tsohon Hakimi


Mai martaba sarkin Katsina, Alhaji Abdulmumini Kabir Usman, ya naɗa sabon sarkin Pauwan Katsina, Hakimin Kanƙara.

Wannan na zuwa ne bayan sarkin ya tsige tsohon hakimin, Alhaji Yusuf Lawal, bayan gano cewa yana taimaka wa yan bindigan da suka addabi jihar.

Sarkin ya naɗa Justice Adamu Bello a matsayin wanda zai maye gurbin Sarkin Pauwan Katsina Hakimin Kanƙara.

Wannan na ƙunshe ne a wani rubutu da Katsina Daily Post ta wallafa a shafinta na kafar sada zumunta Facebook.

Rahoton naɗin ya bayyana cewa Sarkin Labaran Majalisar sarkin Katsina, shine ya tabbatar da wannan sabon naɗin da sarki yayi.

Legit.ng hausa ta kawo muku rahoto cewa bayan gano tsohon hakimin Kankara na da hannu a hare-haren yan Bindiga, majalisar sarkin ta yanke shawarar tumɓuke shi daga muƙaminsa.

A wani labarin kuma Amurka, Burtaniya Sun Bayyana Jimamin Su Kan Mutuwar COAS Ibrahim Attahiru

Ofishin gwamnatin Amurka a Najeriya ya jajantawa yan Najeriya a kan rasuwar shugaban soji tare da wasu sojoji 10 a haɗarin jirgi.

Shugaba Rundunar soji, Ibrahim Attahiru, tare da wasu mutum 10 sun rasa rayuwarsu a hatsarin jirgi ranar Jumu'a 21 ga Mayu.

Source: Legit

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/IM8Uuxtia6qBsdKcEszx7s

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Previous Post Next Post

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/H5IqezEzbfJ3YScTo1dk59

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN