Aljanu biliyan 3 sun karbi Darikar Tijjaniya a Duniya inji Sheikh Dahiru Bauchi


Babban malamin addinin musulunci, Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya yi wata magana wanda ta ba dinbin mabiyansa da sauran al’umma mamaki.

Shehin malamin ya bayyana cewa akwai wasu kebantattun mutane da su ke iya sadu wa da aljanu. Ya ce ya na daga cikin masu mu’amala da su.

Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya ce wasu suna ganinsu, har su yi magana da su, kamar yadda shaidanun mutane su ke hulda da shaidanun Aljanu.

A cewar Sheikh Dahiru Usman Bauchi akwai Aljanu muminai, daga cikin su har mabiya Darikar Tijjaniya wanda yanzu adadinsu ya zarce biliyan uku.

Shehin darikar ya ke cewa daga cikinsu akwai mukaddamai miliyan 200 wadanda su ka yi nisa a Tijjaniya.

Duk da tulin wadannan dakarun Aljanu da suka karbi darikar Tijjaniya, shehin malamin ya ce ba za a rasa wasu dinbin mabiyan da ba a san da zamansu ba.

Dattijon malamin yake cewa suna kokarin ganin an zakulo manyan malamai daga cikin Aljannun da aka ba Darikar Tijjaniya, da nufin yada addini.

Dahiru Usman Bauchi ya ke cewa an kawo shawarar ayi amfani da wadannan rundunar Aljanu domin ceto ‘Yan Tijjaniya daga hannun miyagu a Najeriya.

Ya ce: “Muna shawarar mu nemi alfarmar a yi amfani da su wajen maganin masu zagin Waliyyai, da satar mutane, da ‘yan bindiga da kuma ‘Yan Boko Haram.”

A karshen makon nan, kun ji cewa An zabi Dr. Isa Ali Pantami a matsayin Ministan tarayyar da ya yi fice a shekarar nan ta 2021, an kuma ba shi lambar yabo.

Shigo da tsarin rajistar NIN ya sa mujallar People and Power ta Dr. Isa Pantami ya zama Gwarzon Ministan shekara a lokacin da aka huro wuta ya ajiye aikinsa.

Source: Legit Newspaper


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/IM8Uuxtia6qBsdKcEszx7s

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN