Yanzu Yanzu: Mohammed Adamu ya sauka a hukumance, ya mika mulki ga sabon IGP Usman Baba


Sufeto janar na 'yan sanda mai barin gado (IGP), Mohammed Adamu, ya mika shugabanci ga sabon IGP mai rikon kwarya, Usman Alkali Baba.

A cewar jaridar PM News, an gudanar da bikin mika shugabancin ne a hedikwatar rundunar da ke Abuja a ranar Laraba, 7 ga Afrilu.

Jaridar The Nation wacce ita ma ta ruwaito


rahoton ta bayyana cewa Adamu ya mika mulki bayan Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo ya yiwa Baba ado da sabon mukamin sa a Fadar Gwamnati, Abuja.

Da farko Legit.ng Hausa ta ruwaito cewa mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo, ya yiwa sabon Sifeto Janar na yan sanda kwalliya da karin girma zuwa IGP.

Za ku tuna cewa Shugaba Muhammadu Buhari a ranar Talata ya amince da nadin Usman Alkali Baba a matsayin sabon shugaban yan sanda.


Wadanda ke hallare a bikin kwalliyar sun hada da IGP mai barin gado, Mohammed Adamu; Sakataren gwamnati, Boss Mustapha; da Ministan harkokin yan sanda, Maigari Dingyadi.

Sauran sune Malam Garba Shehu; Laolu Akande; Sakataren fadar shugaban kasa, Tijjani Umar da sakataren ma'aikatar yan sanda.

Source: Legit.ng


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/Cw2uhGNZiIzGM88PV4gpOI

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN