Rundunar yansandan jihar Ogun ta kama wani magidanci xan shekara 49 mai suna Obong Williams Akpan bisa zargin yi wa diyarsa mai shekara 12 fyade sau da yawa.
Yansanda sun kama Akpan ne bayan diyarshi ta kai karar shi da kanta, a ofishin yansanda cewa mahaifinta yana lalata da ita tun tana shekara 5, kuma yanzu ba za ta iya jurewa ba.
Mahaifin yarinyar ya gaya wa yansanda lokacin amsa tambayoyi cewa yana lalata da diyarshi ne saboda mahaifiyarta ta fara tsufa kuma kyaunta ya dusashe.
Yayin tabbatar da lamarin, Kakakin rundunar yansandan jihar Ogun DSP Oyeyemi Abimbola, ta ce tuni aka mika binciken lamarin zuwa sashen yan sandan da ke kula da irin wadannan matsaloli da laifuka a cikin al'umma.
DAGA ISYAKU.COM
https://chat.whatsapp.com/Cw2uhGNZiIzGM88PV4gpOI
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari