Wata babban Kotun jihar Sokoto karkashin mai shari'a Bello Duwale ta daure wani Dan damfara mai suna Hamzat Muhammed Bashar shekara 70 a Kurkuku bayan ta kama shi da laifi a shari'a da aka yanke hukunci ranar Alhamis 1 ga watan Aprilu 2021 ba tare da bashi damar biyan Tara ba.
Alkalin Kotun ya yanke wa Hamzat hukuncin ne bayan ya same shi da laifin damfarar jama'a kudade har adadin N29,865,000.00 .
Hukumar EFCC ta gurfanar da shi a gaban Kotu ranar 7 ga watan Nuwamba 2019 kan tuhuma 12 na damfarar jama'a.
DAGA ISYAKU.COM
https://chat.whatsapp.com/Cw2uhGNZiIzGM88PV4gpOI
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari