Type Here to Get Search Results !

An gurfanar da matar da ta kashe Amarya ta kone gawarta gaban Kotu


Wata Kotun Majistare a Birnin Minna na jihar Niger ta tasa keyar Amina Aliyu tare da wasu yan mata guda uku bisa zargin kashe Amarya da mijinta ya aura.

Ana zargin Amina Aliyu ta hada baki da kawayenta ta kashe Amaryar da mijinta ya auro Fatima Aliyu, ranar Talata 23 ga watan Maris, makonni bakwai bayan aurensu.

Yansanda sun gurfanar da Uwargida Amina wacce ke renon jariri mai mako uku da haihuwa a gaban Alkali tare da wasu yan mata uku, Aisha Mohammed, Zainab Aliyu da Fauziyya Rabi’u ranar Laraba 31 ga watan Maris.

Mai gabatar da kara na yansanda ASP Ahmed Daudu Kwangoma, ya shaida wa Kotu cewa Amina ta hada baki tare da wadanda aka gurfanar gaban Kotu, suka je gidan Fatima, inda Amina ta yi amfani da tabarya ta doke ta a kai, lamari da ya sa Fatima ta suma ta fadi a kasa a cikin Kicin na gidanta.

Daga bisani suka jawota zuwa cikin palon gidan suka banka wa jikinta wuta, lamari da ya yi sanadin mutuwarta.

Alkalin Kotun ya yi umarni da tasa keyar Amina Aliyu da A’isha Aliyu zuwa gidan gyara hali na Minna yayin da aka kai Zainab Aliyu da Fauziyya Rabi’u gidan kula da kangararrun yara da ke Minna kafin sake zaman Kotu na gaba.

Kotu ta dage sauraron shari'ar har zuwa ranar 27 ga watan Aprilu 2021.


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/Cw2uhGNZiIzGM88PV4gpOI

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Post a Comment

0 Comments
* Please Don't Spam Here. All the Comments are Reviewed by Admin.

Top Post Ad

Hollywood Movies