Ina Dab Da Kashe Kaina Saboda Kuncin Rayuwa – Ummi Zee ZeeKu tayani da addu’a, ina cikin kangin rayuwa har ina ji kamar na kashe kaina, Ummi Zeezee

Fitacciyar tsohuwar jarumar masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, Ummi Ibrahim, wacce aka fi sani da Ummi Zeezee, ta ce ta shiga kangin rayuwa, inda har ta kan ji kamar ta kashe kanta.

A ranar Asabar, 3 ga watan Afrilu ne jarumar ta fadi hakan a wani sako da ta wallafa a shafinta na Instagram.
Ta ce: “A ‘yan kwanakin nan, na shiga matsanancin kuncin rayuwa, ta yadda har na kan ji ina so na kashe kaina.”

Sai dai jarumar wacce ta yi fitattun fina-finai irinsu ”Jinsi,” “Gambiza” da “Tutar So” ta ce kada kowa ya tambaye ta dalilin da ya sa take so ta aikata wannan danyen aiki.
Ta kara da cewa “Amma don Allah kada kowa ya tambaye ni dalili me ya sa, abin da nake bukata a gare ku shi ne, addu’a.”

Leadership ayau


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/Cw2uhGNZiIzGM88PV4gpOI

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN