An yi kuskuren tura mata N456m, ita kuma ta sayi gida da mota


Wata mata daga Lousiana da aka bayyana da suna Kelyn Spadoni ta tsinci kanta cikin matsala bayan da ta ki mayar da dala miliyan 1.2 (N456,600,000) wanda aka yi kuskuren turawa ta asusun ajiyarta na banki.

An ruwaito cewa lamarin ya faru ne a watan Fabrairu, kuma an ce matar ta yi biris da kira, sakonni da imel daga bankin.


Ta shiga matsala: An yi kuskuren tura mata N456m, ita kuma ta sayi gida da mota

Spadoni, mai tura sakon 911, ta yi sauri ta sayi gida da mota a ranar da ta ga kudin a cikin asusun ajiyarta.

Yanzu, kamfanin dillanci na matar, Charles Schwab, na neman ta mayar da cikakken kudin saboda an tura mata da kudin ne bisa kuskure saboda matsalar na’ura mai kwakwalwa.

Da farko dai kamfanin ya tura ma Spadoni $ 82 (N31,201), amma bankin ya ya yi kuskuren tura $ 1.2 (N456,600,000) zuwa asusun ta saboda matsalar na’ura.

Charles Schwab ya kai wannan matashiyar kotu inda ya gurfanar da shi saboda ta ki mayar wa kamfanin kudin.

Sun kuma yi korafin cewa tun daga farko ta sanya hannu a yarjejeniyar da ke cewa kwastomomi su mayarwa da kamfanin kudaden da aka biya ya zarta.

Kakakin ofishin Jefferson Parish sheriff ya ce:

“Ba ta da wani hakki na doka a kan wannan kudin ko da kuwa an shigar da ita a wurin ne bisa kuskure. Kuskuren lissafi ne.”

An kama Spadoni ne a ranar 7 ga Afrilu kuma an sake ta a kan kudi N149,812.73.

A kan wannan, kamfanin ya kuma karbe gida da motar da ta saya kuma ana sa ran za ta biya cikakken kudin da ya hau ko zaman shekaru a gidan yari.

An kuma kore ta daga aikin ta na tura sakon 911.

A wani labarin, mun ji cewa sama da mutane 100, 000 su ka fice daga garin Damasak, jihar Borno, su ka tsallaka Jamhuriyyar Nijar.

A ranar Laraba, 14 ga watan Afrilu, 2021, ‘yan ta’addan kungiyar Boko Haram su ka sake kai hari wanda shi ne na shida a cikin kwana goma a garin Damasak.

Boko Haram sun addabi babban birnin na karamar hukumar Mobbar a ‘yan kwanakin nan, hakan ya yi sanadiyyar da mutane su ka yi gudun hijira zuwa Nijar.

Source: Legit.ng


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/Cw2uhGNZiIzGM88PV4gpOI

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN