Mahaifiyar amarya ta tsere da sadakin diyarta, ta bar madaura aure cikin mamaki


An yi wata karamar hatsaniya wurin biyan sadaki bayan an gano cewa mahaifiyar amarya tayi sama da fadi da kudin sadakin da sirikanta suka kai.

Mahaifiyar amaryar mai suna Anne Maweni, an gano cewa ta yi tsammanin iyayen amaryan zasu yi mata mugunta, lamarin da yasa ta tsere da sadakin da ya kai Sh170,000.

An fara shirin auren a Garsen, yankin Tana River dake Kenya yayin da 'yan uwa suka cewa, Maweni, mahaifiyar amaryar bata nan, The Nation ta ruwaito.

"Da aka fara bikin, ita ta baiwa baki da dattawa abinci amma sai bata zauna tare da su ba. babu wanda ya san lokacin da ta gudu," Veronica Meily, 'yar uwar Maweni ta sanar.

Duk kokarin samunta da aka yi a waya ya gagara saboda wayarta a kashe take.

Daga bisani Maweni ta tura sakon kar ta kwana ga kanwarta ta wata lamba inda tace ta jagoranci daurin auren da bikin. Daga nan ne dattawa da sirikan dake zaune suka gane cewa akwai wata matsala.

Daga bisani Maweni ta sanar da cewa tayi hakan ne saboda sun bar ta da 'ya'yan bayan rasuwar mahaifinsu kuma babu mataimaki, amma aure ya tashi sun zo kwasar rabonsu.

Source: Legit


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/Cw2uhGNZiIzGM88PV4gpOI

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Previous Post Next Post
Latsa nan ka shiga group din mu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

Domin zama Wakilin mu a garin ku LATSA NAN