Sokoto: Yan bindiga sun kashe Alhaji Rabi'u Amarawa, da mutane 12 bayan sun karbi N5m


Yan bindiga sun kashe Alhaji Rabi'u Amarawa bayan sun karbi kudin fansa har N5m a wajensa. Wasu yan bindiga sun dauke dan kasuwan ne ranar Litinin a jihar Sokoto.

Mutum 12 suka rasa rayukansu garin ceto Alhaji Rabi'u lokacin da yan bindigan suka dauke shi, cikin su har da kaninsa.

Daily Trust ta labarta cewa yan bindigan sun farmaki al'umma ne suka dauke Rabi'u, da misalin karfe 2 na dare ranar Litinin. Sakamakon haka jama'a suka yi gangami tare da Yan Banga suka bi su, sai dai Yan bindigan sun buda masu wuta lokacin da suka kula jama' sun biyo su. Lamari da ya yi sanadin mutuwar mutane 12 ciki har da kanin Alhaji Rabi'u.


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/HUEzyk9QvHZ6kSk4bH2U6K

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Post a Comment

Please Select Embedded Mode To Show The Comment System.*

Previous Post Next Post
Latsa nan ka shiga group din mu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

Domin zama Wakilin mu a garin ku LATSA NAN