Yan bindiga sun farmaki kauyen Mussuru a karamar hukumar Danko-Wasagu suka sace mutane 5 suka raunata mutum biyu da misalin karfe 11 na dare ranar Juma'a.
Wannan Yana faruwa ne a karo na biyu kasa da mako daya bayan yan bindiga sun sace wata matar aure a kauyen na Mussuru
Mussuru na iyaka da karamar hukumar Maru a jihar Zamfara, kuma tana karkashin Mazabar Dan Umaru a garin Bena da ke karamar hukumar Danko-Wasagu a jihar Kebbi.
Majiyarmu ta yi zargin cewa Yan bindigan sun sace mutum 5. Mata guda 3 da maza guda 2, Cikin wadanda aka sace har da matan Dagacin garin su 2, kuma suka raunata mutum 2.
Wadan da ake zargin an sace su ne:
1 Rashida Ahmed Maiunguwa
2 Shafa'atu Ahmed Maiunguwa
3 Hannatu Abdullahi
4 Danlami Sale
5 Hamidu Dadi
Wadanda aka raunata:
1 Ummaru Danbaba
2 Mamuda.
Yanzu haka wadanda aka raunata suna jinya a babban Asibitin garin Bena inda ake rade radin cewa watakila a turasu zuwa Assibitin UDUTH da ke Sokoto.
Majiyar mu ta yi zargin cewa Yan sanda guda biyu da ke kauyen Mussuru sun kasa iya fuskantar Yan bindigan da suka zarce su a yawa..
DAGA ISYAKU.COM
https://chat.whatsapp.com/HUEzyk9QvHZ6kSk4bH2U6K
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari