Kebbi: Yadda Yan bindiga suka farmaki garin Birnin kebbi suka sace budurwa


Da sanyin safiyar ranar Juma'a Yan bindiga sun farmaki unguwar gangaren NEPA, Tudun Wada, da ke garin Birnin kebbi suka yi awon gaba da wata budurwa mai shekara 18 a Duniya. Kakakin hukumar yansandan jihar Kebbi DSP Nafiu Abubakar ya tabbatar da faruwar lamarin.

Mun samo cewa  hukumar yansandan jihar Kebbi ta dukufa wajen ceto budurwa da yan bindigan suka sace.

Kazalika, mun tattaro cewa mahaifin yarinyar da aka sace mai suna Faruk Muhammed jami'in rundunar NSCDC na jihar Kebbi ne.

Ya gaya wa manema labarai cewa Yan bindigan sun je unguwar ne suka fara ayyukansu.

A cewar mahaifin yarinyar da Yan bindigan suka dauke "Sun iso gidana, sai na fahimci cewa akwai matsala, sakamakon motsi da naji da bai kamata ba,  Akwai hanyoyin fita daga gidana guda biyu.

Sai na yanke shawarar cewa mu fita ta kofar garejin mota,  Amma fitar mu ke da wuya ta wannan kofa sai muka yi arba da wani Dan bindiga dauke da makami, sai muka koma muka ketare ta gidan makwabta..

Yan bindigan sun balle gidana suka shiga suka fara bincike daki zuwa daki, sun tarar da diyata tana barci a cikin dakinta, sai suka dauke ta suka tafi da ita".

Wata majiya ta ce Yan bindigan sun farmaki gidan wani mutum mai suna Malam.Sanusi Nagoru wanda ya dambace Yan bindigan guda biyu kuma ya yi galaba a kansu, sai dai ya kasa samun taimako daga jama'a lokacin da yake dauki ba dadi da Yan bindigan, daga bisani ya tsere ala tilas domin ya tsira da rayuwarsa 

"Lokacin da ya gan sauran Yan bindigan sun nufato shi domin su taimaka wa yanuwansu lokacin da yake dambace su, sai ya yi watsi da su ya shige gida ya rufe kofar gida.

Daya daga cikin matarsa ta dakile kofar gidan domin hana Yan bindigan shiga gidan, amma sai Yan bindigan suka buda wa kofar gidan wuta da bindiga, sakamakon haka harsashi ya huda kofar ya sami matar a cinya, wanda ya yi sanadin kai ta Asibiti a garin Birnin kebbi inda take samun kulawan ma'aikatan lafiya". A cewar majiyar


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/HUEzyk9QvHZ6kSk4bH2U6K

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN