Sojojin Myanmar sun hamɓarar da shugabar da ta goyi bayan yi wa musulman Rohingya kisan kiyashi


Shafin BBCHausa ta wallafa cewa Sojoji a Myanmar sun kifar da gwamnatin shugabar ƙasar Aung San Suu Kyi, kamar yadda wata sanarwa da rundunar sojin ƙasar ta fitar ta tabbatar.

Kakakin jam'iyya mai mulki ta National League for Democracy wato (Nasr) ya tabbatar da cewa yanzu haka tsohuwar shugabar na tsare a hannun sojoji, tare da wasu manyan ƴan majalisar zartarwarta.

A halin da ake ciki dai ƙasar na tsaka da fama da tankiya tsakanin gwamnatin farar hula da jagororin soja da ke zargin cewa ana tafiyar da al'amura ba daidai ba.

Hatta a zaɓen watan Nuwamban bara, jam'iyyar shugabar ta samu isassun kujeru domin kafa gwamnati, amma sojoji sun kafe a kan cewa an yi magudi a zaɓen.

Har zuwa shakearar 2011 sojoji ne ke mulkin Myanmar, kafin daga bisani farar hula suka karba.

Da ma can Shugaba Suu Kyi ta taɓa kwashe tsawon shekaru a tsare.

Wanne hali ake ciki a yanzu?

Min Aung Hlaing

Sanarwar rundunar sojin ta ce an mika mulki ga babban kwamandan sojin ƙasar mai suna Min Aung Hlaing nan take ba tare da ɓata wani lokaci ba.

Gidajen rediyo da talabijin na kasar na a kashe, kuma an katse layukan waya da na intanet.

Ana iya hango sojoji na ta faman sintiri fuskokinsu a murtuƙe, a kan titunan babban birnin kasar Naypyitaw da kuma babban birnin Yangon.

Bayanan da muka samu na baya bayan nan na tabbatar da cewa sojojin da suka yi wannan juyin mulki sun kafa dokar ta ɓaci a sassan ƙsar baki ɗaya.

Kamata ya yi majalisar dokokin ƙasar ta sake zama don tsawaita wa'adin shugabar da aka hambarar, amma yanzu sai dai kawai ace yadda sojojin suka dama haka za a sha.


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/LKeYYgwzLbW8DdHbjNuEos

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN