Boko Haram sun kashe 'yan sanda 2, sun sace 2 a Borno


Jaridar legit ta wallafa cewa wasu da ake zargin 'yan Boko Haram ne sun afka Chabal da wasu anguwanni dake karkashin karamar hukumar Magumeri a ranar Lahadi da rana sannan sun kashe wasu 'yan sanda guda biyu kafin su yi garkuwa da wasu biyu.

Kamar yadda wasu suka sanar da Vanguard, 'yan ta'addan sun kwace wasu motocin sintiri guda biyu sannan suka banka wa daya wuta a hanyar Maiduguri-Chabal-Magumeri titi mai tsawon 35km arewa da babban birnin jihar.

Al'amarin ya faru ne bayan sababbin hafsoshin sojin Najeriya da sun kai ziyara Maiduguri, inda suka kai wa gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum ziyara da Shehun Borno, Abubakar Garbai Elkanemi don neman hadin kansu wurin kawo karshen rikici a jihar.

Sai ga 'yan ta'adda sun kai farmaki jihar a yau Lahadi.


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/LKeYYgwzLbW8DdHbjNuEos

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN