Rikicin Oyo: Mutum 10 sun mutu, 70 sun sami raunukan bindiga, yan arewa 30 sun bace


An kashe akalla mutum 10, mutum 70 sun sami raunukan bindiga kuma yan arewa guda 30 sun bace sakamakon wani mumunan farmakin tashin hankali da ya auku a kasuwar Sasa da ke karamara hukumar Akinyeli a jihar Oyo, Jaridar DailyNigerian ta ruwaito.

Kazalika DailyNigerian ta ce akalla mutane 6000, akasari Hausawa, sun nemi mafaka a gidan Sarkin Sasa Alhaji Haruna Maiyasin.

Alhaji Maiyasin ya shaida wa DailyNigerian cewa "Akwai fiye da mutum 6000 cakude a gidana. An kashe mutane da dama, yayin da aka raunata jama'a da dama".

Jaridar ta kara da cewa wani ganau ya ce lamarin ya samo asali ne ranar Alhamis, lokacin da wani dan dako ya dauko kwandon tumatir, kuma cikin kuskure ya banke wata mata Bayarba, sai ta rama kuma ta Kira matasa yan iska yan kabilar Yarbawa, lamarin da ya kai ga ba hammuta iska. Sai dai bayan da aka yi fadan ne, sai daya daga cikin yan iskan da matar ta kira ya mutu a Asibiti.

Ana zargin cewa bayan da labarin mutuwar ta yadu, sai matasa Yarbawa suka bazama suka fara kai wa yan kasuwa yan arewa hari. 

A wata tattaunawa da DailyNigerian, shugaban yan kasuwa na kasuwar Sasa Usman Yako, ya ce sun gaya wa yansanda cewa daya daga cikin yan iska da Bayarban ta Kira suka yi fada a kasuwan ya mutu, amma ya yi zargin cewa yansanda basu yi azama wajen kai dauki ba, har sai da lamarin ya kazamce.

Ya kara da cewa " Lokacin da yan Amotekun suka iso wajen, sai suka fara harbin yan arewa, yayin da yan iska suka fara cinna wa shaguna da gidajen Hausawa wuta tare da harbin Hausawa.

Bisa ga dukkan alamu an shirya wannan ta'asa ne domin a kai wa yan arewa farmaki".

"Farmakin ya bazu zuwa babban tagwayen hanyar mota ta Lagos zuwa Ojo, an kone motocin Tilera na yan arewa masu yawa makare da kayakin, aka yi wasoson dukiyoyin da suka dauko, kuma aka yi wa direbobin motocin yankan rago" a cewa Usaman Yako.


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/HUEzyk9QvHZ6kSk4bH2U6K

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN