Kebbi: Yan bindiga sun kashe mutane, sun sace shanaye a karamar hukumar Danko-Wasagu


Rahotanni daga Masarautar Zuru da ke kudancin jihar Kebbi sun ce Yan bindiga sun kai farmaki a kauyukan Ganyale da Doka da ke karkashin garin Unashi a karamar hukumar Danko/Wasagu da yammacin ranar Litinin 22/02/2021.

Yan bindigan sun yi awon gaba da shanaye, bayan sun halaka mutane tare da raunata wasu .

Sai dai mun samo cewa soji tare da taimakon Yan sa Kai, sun fuskanci Yan bindigan a yankin kauyukan Yababa, Cedkkubu da  Doka.

Wannan harin na Litinin yana zuwa ne bayan harin Yan bindiga da ya yi sanadin kashe mutum 2, tare da sace mutane 9 mako da ya gabata a kauyen Jambali, da ke kusa da garin Bena.


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/HUEzyk9QvHZ6kSk4bH2U6K

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN