Wata gawa ta bace a dakin ajiye gawa, an kama mai gadi


Rundunar yansandan jihar Delta ta kama mai gadin gidan ajiye gawa a garin Oghara da ke jihar Delta sakamakon bacewar gawar wata mata Patience Amughoro mai shekara 58 a Duniya kafin mutuwarta.

Matar ta mutu ne shekara da ta gabata, kuma aka adana gawarta a dakin ajiye gawa wani Asibiti mai zaman kanta da ke garin Oghara 

Ranar Asabar 20 ga watan Fabrairu 2021, iyalan matar sun isa dakin ajiye gawar domin su karbi gawar Mrs. Patiens domin su bizine ta..Sai dai an kawo masu gawar wata mata daban.

Sakamakon  haka ne ya sa iyalinta suka kai kara wajen yansanda. Daga bisani yansanda suka kama mai gadin gidan ajiye gawa.


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/HUEzyk9QvHZ6kSk4bH2U6K

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Previous Post Next Post

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/J8ryqryDtwR9yvxrOOBlJU

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN