Goodluck Jonathan: Wasu 'yan Najeriya ba sa son ya sake tsayawa takara


Wasu 'yan Najeriya na cewa bai kamata tsohon Shugaban Ƙasar Goodluck Ebele Jonathan ya sake tsayawa takara ba, yayin da aka ci gaba da raɗe-raɗin cewa jam'iyyar APC mai mulki za ta tsayar da shi a zaɓe mai zuwa. Shafin BBCHausa ta ruwaito.

Da safiyar Litinin ce aka tashi da sabuwar jita-jitar cewa jam'iyyar APC mai mulki na shirin tsayar da Jonathan ɗin a matsayin ɗan takararta a zaɓen shugaban ƙasa mai zuwa tare da Gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai a matsayin mataimaki.

Sai dai Jonathan da APC da El-Rufai, waɗanda abin ya shafa, ba su ce komai ba game da labarin, amma kamar yadda aka saba 'yan Najeriya sun yi ta amfani da shafukan zumunta domin goyon baya ko akasin haka.

Cikin wata hira da BBC a kwanakin baya, shugaban jam'iyyar APC na riƙo a matakin ƙasa, Mai Mala Buni ya musanta batun cewa suna shirin tsayar da tsohon shugaban takara.

Duk da cewa babu wata ƙwaƙƙwarar majiya da ta tabbatar da labarin, wasu na goyon bayan hakan, yayin da wasu ke cewa bai kamata tsohon shugaban ya dawo fagen mulki ba.

Abin da 'yan Najeriya ke cewa

Goodluck Ebele Jonathan da Muhammadu Buhari

Sunan 'Jonathan' na cikin maudu'an da aka fi magana a kansu a sararin Najeriya na dandalin Twitter, inda aka yi amfani da shi sau 63,500 ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoton - duk da cewa ba shi kaɗai ne Jonathan ɗin da ake magana a kai ba.

Shi ma sunan El-Rufai, an tattauna a kansa sau 9,276 ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoton.

Wata mai suna @firstladyship ta ce "Ina maimaitawa, ni masoyiyar Jonathan ce amma in dai jita-jitar nan ta zama gaskiya...ba wai daina sonsa zan yi ba kawai, zan yaƙi siyasarsa sosai. Ya kamata Jonthan ya ci gaba da jin daɗin ritayarsa."

Kauce wa Twitter, 1

Karshen labarin da aka sa a Twitter, 1

Ita ma @MattBobmanuel cewa ta yi "Idan Jonthan ya yarda zai yi takara tare da El-Rufai to bai cika mutumin da muke tunani ba".

Kauce wa Twitter, 2

Karshen labarin da aka sa a Twitter, 2

"Ya kamata Jonathan ya ci gaba da rayuwarsa ƙasa-ƙasa tare da jin daɗin abin da ya rage na rayuwarsa," a cewar @iamObiii.

Kauce wa Twitter, 3

Karshen labarin da aka sa a Twitter, 3

'Ba ma zawarcin Jonathan'

Mai Mala Buni
Bayanan hoto,

Gwamnan Jihar Yobe Mai Mala Buni, shi ne shugaban riƙo na ƙasa na jam'iyyar APC

A farkon watan Fabarairu ne wasu rahotanni suka ce wasu gwamnonin APC daga arewacin na ƙulla yadda za a yi Goodluck Jonathan ya samu takarar domin dama ɗaya kawai yake da ita ta yin shugabanci na shekara huɗu, inda daga nan sai mulki ya sake komawa arewa.

Sai dai jam'iyyar ta ce wasu ne kawai suke ƙirƙirar irin wannan labari, wanda babu ƙamshin gaskiya a cikinsa.

Mai Mala Buni, shi ne shugaban riƙo na jam'iyyar APC, kuma gwamnan Jihar Yobe, ya shaida wa BBC cewa babu wannan maganar.

"Ba maganar wani zawarcin Jonathan a halin da ake ciki, wataƙila waɗanda suke irin waɗannan maganganu tsoro ne a zukatansu," in ji shi.

"Ko da mutum na son kafa hujja ne da ziyarar da muka kai masa yayin bikin zagayowar ranar haihuwarsa, to mun je ne a matsayinsa na tsohon shugaban Najeriya don haka ziyararmu ba ta da wata alaƙa da siyasa.

Rahotun shafin BBCHausa


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/HUEzyk9QvHZ6kSk4bH2U6K

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN