Auren shekara 20 da yara 3, maigida ya kashe matarsa da wuka, duba dalili


Rundunar yansandan jihar Ogun ta kama wani magidanci mai suna Sobola Olatunji bayan ya caka wa matarsa wuka sakamakon haka ta mutu.

Sabola wanda ma'aikacin karamar hukumar Remo ta arewa ne, ya kashe matarsa mai suna  Momudat Sobola ne, lokacin da suke fada, lamari da ya samo asali daga zargin da Sabola ya yi cewa matarsa tana hulda da bai dace ba da wasu maza bayan ya gan wasu sakonni a wayar salula na matarsa. A lokacin da Sabola ke fada da matarsa ne, sai ya dauko wuka ya caka wa matarsa a baya.

Mahaifin matarsa Momudat Alhaji Ambali Yinusa ne ya kai kara a ofishin yansanda na Owode-Egba wanda suka je gidan suka kama Sabola.

An garzaya zuwa Asibiti da matar, amma sai ta mutu yayin da Likita ke kokarin ceto rayuwarta.

Ma'auratan sun shade shekaru 20 suna zaman aure tare da samun albarkan haihuwan yara uku kafin aukuwan lamarin.

Kakakin yansandan jihar Ogun  DSP Abimbola Oyeyemi ta tabbatar da faruwar lamarin. Yansanda na ci gaba da gudanar da bincike.


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/HUEzyk9QvHZ6kSk4bH2U6K

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN