Yan bindiga sun kashe yansanda biyu, kuma suka banka wuta, lokacin wani farmakin bazata da suka kai a wani ofishin yansanda a garin Aba da ke jihar Abia ranar Talata 23 ga watan Fabrairu.
Rahotanni sun ce yan bindigan sun fasa dakin ajiye makamai a ofishin suka yi awon gaba da makamai bayan sun kashe Jami'in da sanda mai mukamin superintendent da kuma wani mai mukamin kofur (Police Corporal)
Daily trust ta ruwaito cewa yansanda sun takaita zirga zirga a kusa da ofishin yansanda da yan bindigan suka kone, lamari da ya kara haifar da cinkoson ababen hawa a wajen.
DAGA ISYAKU.COM
https://chat.whatsapp.com/HUEzyk9QvHZ6kSk4bH2U6K
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari