Cuta da magani: Duba amfanin Kanumfari a jikin mutum (2)


Amfanin Kanumfari ga matsalolin Tari ko Asthma wannan a bayyane ne yake, masamman ma da yake yana da saukaka radadin ciwon makogwaro, da majinar da take kwararowa mutum, ko wacce ta makale masa a kirji, idan ana son a kawar da matsalolin da suka shafi bangaren numfashi ana iya nika shi a sa a ruwa na tsawon minti 10 sannan a sha, amma lallai ya kasance likita ya san da haka, domin in mutum yana da mummunar Asthma ba a ba shi shawarar bin wata hanya ta magani in ba tare da sanin shi likitan nasa ba, amma fa inda za a tauna kwayoyin Tafarnuwan za a iya kawar da doyin ko kuma warin numfashi, a yi maganin radadin Hakori sannan kuma a magance Tari da radadin makogwaro, koda yake wuce gona da iri a kansa ya kan janyo lalacewar dasashi.

(5) Kanumfari ya kan magance matsalolin Tumbi ko ( Ciki ) ta hanyar da yakw markade abinci, yakan kuma yi maganin kumburin ciki, ya kawara da ko maganin da wahalar da ake sha wajen markade shi abinci, ya kan kuma yi maganin amai ya kuma rage yiyuwar kamuwa da gudanawa, sananne ne ga masu juna biyu yadda wani lokaci su kan ci karo da rikicewar ciki, da ma cutar Atini, to saboda shi sinadarin Fibres din dake cikin Kanumfarin sau da yawa sai ayi sa’a ya yi maganin. Bugu da kari kuma yawan yin kumallon safiya da maraice, da masu juna biyun suke yi, domin an san su da yin aka yana raguwa.

Kanumfari kan saukaka yawan kumburin ciki wanda za ka ji mutum da ga karshe yana ta yin hutu ko Tusa, masana sun bayyana cewa shi Kanumfarin kan rage matsalar Ulcer (gyambon ciki) ya kuma ba wa mutum damar cin abinci kamar yadda ya kamata. Kanumfarin zai iya kawar da matsalolin ciki, ya sanyaya shi, masamman ma ta wurin shan shayin sa, nan take in cikin ya kumbura in dai za a sha shi sai ka ga ya sa an samu sauki, ya bulbular da yawun da zai taimaka wajen markade abinci, kamar yadda zai taimaka wajen kashe kwayoyin Bacteria da za su rikita Tumbi gaba daya wadanda kuma daga karshe suna sanadiyar kamuwa da wata cuta.

(6) Har ma da cutar Kansa (dahi) dinnan da ake fama da ita Kanumfarin ya kan taimaka, wasu binciken da aka yi a wasu wuraren da dan Adam ya yi an gano cewa Kanumfarin ya kan taimaka wajen yin rigakafin kamuwa da cutar Daji ko kansa, masamman ma ta Huhu, man Eugenol da yake cikin Kanumfarin ya kan taimaka wajen samun kariya daga kamuwa da cutar Kansa din, da asalin ta ya samu ne sakamakon sinadaren kere-keren zamani wadanda suke sa su illata kayayyakin cikin mutum, sai dai kuma duk da haka dole a tsoratar da kanana yara saboda kuwa, domin cikin sauki zai iya haifar masu da matsalar rama ko kuma cutar Hanta.

(7) Akan yi aiki da Kanumfarin don rage kiba, don yana da Antiodidants wanda yake taimakawa wajen yin hakan, wasu masanan suna cewa in aka sa shi a gaba kawai za a iya rage nauyin Kilo daya zuwa kilo da rabi a duk mako, wannan in dai har za a kiyaye tsarin cin abincin da yake da Antiodidants ke nan, kuma da karancin Calories, bincike- bincike daga jami’o’in Turai daban-daban sun tabbatar da cewa Kanumfari ya fi sauran abinci wadatar Antiodidants a cikin sa kamar dai irin su Fenolic acids.

Rahotun Jaridar Leadership


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/HUEzyk9QvHZ6kSk4bH2U6K

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN