An kashe wani mutum aka banka wa gawarsa wuta a Yola, duba dalili


Rundunar ‘yan sanda a Adamawa, a ranar Lahadi, ta tabbatar da mutuwar wani da ake zargi da zama mamba a wata kungiyar gungun masu laifi da aka fi sani da‘ Shila Boys' a Jimeta, karamar hukumar Yola ta Arewa. Jaridar legit hausa ta ruwaito.

Wasu ‘yan zanga-zanga sun kona dan kungiyar Shila har lahira bisa zargin cewa ya yi wa wata mata sata da kuma daba mata wuka, Daily Trust ta ruwaito.

Jami'in hulda da jama'a na 'yan sanda a jihar, DSP, Sulaiman Nguroje, ya tabbatar da hakan ga Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) a ranar Lahadi a Yola.

Nguroje ya ce lamarin ya faru ne a ranar Asabar da misalin karfe 7:00 na dare.

Ya ce an dauki gawar wanda ake zargin ne daga rundunar Jimeta da ke Jimeta.

Ya fadawa NAN cewa mambobin kungiyar su uku, suna kan keke ne yayin da suka yi wa matar fashin a hanyar Mubi da ke Jimeta.

“Matar (an sakaya sunanta) ta yi ihu don neman taimako kuma nan take, wasu fusatattun mutane suka bi wadanda ake zargin, suka kama daya daga cikinsu suka cinna masa wuta.

“Sauran 'yan kungiyar biyu kuwa, sun tsere,’’ Nguroje ya fada wa NAN.

A wani labarin, Rundunar ‘yan sanda a jihar Kaduna ta samu nasarar cafke wasu masu satar mota su biyu a yankin Nassarawa na babbar hanyar Nnamdi Azikiwe da aka fi sani da Western bypass, Daily Trust ta ruwaito.

‘Yan sanda sun kuma gano karamar mota kirar Toyota Camry dauke da lambar rajista ABC 590 DX da Toyota Corolla mai launin toka dauke da lambar rajista KTN 304 AG, daga wadanda ake zargin.


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/HUEzyk9QvHZ6kSk4bH2U6K

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN