Rundunar yansandan jihar Lagos ta kama wani farar hula direban motar yansanda na sashen Federal Investigation Bureau, Special Tactical Squad da ke Lagos mai suna Waheed Adewale bisa zargin yunkurin sayar da mota da ya sace da karfin bindiga a jihar Lagos.
Ana zargin Mr Adewale ya sace motar ne a Lagos, sai dai an kama shi ne a garin Osogbo yayin da yake neman wanda zai saye motar a jihar Osun.
Kwamishinan yansandan jihar Osun Wale Olokode, ya ce an kama Waheed ne yayin da yake kokarin neman wanda zai saye motar ranar 20 ga watan Janairu 2021.
https://chat.whatsapp.com/LKeYYgwzLbW8DdHbjNuEos
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari