Wata mata mai shekaru 91 a duniya ta auri sahibinta, wani mutum mai shekaru 73 bayan shafe shekaru fiye da 10 suna soyayya, rahoton jaridar The Nation. Jaridar legit hausa ta ruwaito.
An kuma gwangwaje biki na kece raini a ranar daurin auren na su.
Matar mai suna Evelina Meadder ta auri saurayinta da suka dade tare mai suna Calgent Wilson mai shekaru 73 a wani babban biki da aka shirya a kasar Jamaica.
A cewar rahoton da The Mirror ta wallafa, ma'auratan sun fara soyayya ne tun a shekarar 2009 a lokacin da Evelina ta kamu da rashin lafiya, shi kuma Calgent, manomi, ya yi jinyarta har zuwa lokacin da ta warke.
Evelina ta ce sun daga lokacin suka shaku, ya kan mata maganar cewa ya kamata su yi aure amma a lokacin da ya ke shan barasa ne sai kawai ta yi dariya ta yi watsi da zancen.
Daga karshe dai sun yi auren kuma muna musu fatan alheri.
https://chat.whatsapp.com/HUEzyk9QvHZ6kSk4bH2U6K
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari