Yara Almajirai guda uku tare da wasu mutum takwas sun kone kurmus har lahira, bayan wata mota tankar mai ta yi bindiga kuma ta kama da wuta a Gawu da ke babban Birnin tarayyar Najeriya Abuja, Jaridar Daily trust ta ruwaito.
Jaridar ta ce wadanda suka mutu a wannan ibtila'i sun hada da wata matar aure mai suna Halima Mohammed Yusuf, da shugaban kungiyar Banga ta Gawu, Adamu Ibrahim, da Dantala Usman, Umar Aliyu, Mohammed Hamza, Hassan Usman, Gambo Hamisu tare da Sani Abdulmutalib.
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/HUEzyk9QvHZ6kSk4bH2U6K
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Wani ganau ba jiyau ba ya ce " Motar tankar mai ta fito daga gefen Lapai zuwa Izzom, amma garin kokarin kauce wa yin karo da Tileran motar Dangote saboda kokarin kauce wa rami, sai motar ta kwace wa Direba ta kauce kan titi ta je ta yi karo, sakamakon haka motar ta fadi man petur ya yi ta malala.
Ganin haka ya sa mutane suka je wajen da bokitai da jarkoki suka yi ta diban mai, ana cikin haka ne wata matar aure mai suna Halima ta je wajen, domin ta kori danta daga cikin masu diban mai, sai dà i tsautsayi ya riga fata, domin dai kwatsam sai wuta ta tashi a wajen nà n take ta kone Halima da sauran jama'a da ke wajen.
DAGA ISYAKU.COM
https://chat.whatsapp.com/HUEzyk9QvHZ6kSk4bH2U6K
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari