Za a kashe kurtun soji ta harbi da bindiga bàyan ya kashe wani hafsan soji


Wata labarta cewa wata Kotun soji da ke zamanta a barikin sojin musamman na Maimalari da ke Borno ta yanke ma wani kurtun sojimai suna Azunna Maduabuchi hukuncin kisa ta hanyar harbe shi da bindiga har lahira sakamakon kashe wani hafsan soji Mai suna Lt. Babakaka Ngorgi.

Sahara Reporters ta ruwaito cewa marigayi Lt. Babakaka yana tsakar waya da sabuwar Amaryarsa wacce ya Angonce da ita ba da dadewa ba, kwatsam sai kurtun soji Azunna ya auna shi a kiji ya harbe shi da bindigarsa har sau biyar, lamari da ya sa hafsan ya mutu nan take a barikin soji na 202 sashen sojin musamman na 21 na sojin surke da ke Bama.

Jaridar ka kuma labarta cewa kurtun sojin ya dade yana kuka da cewa an rufe asusun ajiyarsa na Banki, sakamakon haka baya iya zarar kudin albashinsa balle alawus, sakamakon haka lamura suka yi masa wuya kasancewa ba a baahi izinin tafiya ba.

Ta kuma ce bayan kurtun sojin ya kashe hafsan sojin, lamari da ya jefa sauran hafsoshi da kuratan soji cikin mamaki, wasu kuratan soji sun fusata kuma suka nemi su je dakin da ake kulle masu laifi domin su kashe ahi ta hanyar bindige ahi har lahira amma babban Kwamandan bataliyan ya hana su.


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/J9zhUeQqg52KIxyFnYByJN

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN