Yanzu yanzu: Matasa sun kone babban mota makare da shanu sakamakon buge wani yaro


Wasu fusatattun matasa a garin Saki, jihar Oyo, sun babbaka mota dauke da dabbobi sakamakon buge wani yaro mai suna, Ayuba Raji, da motar tayi, Sahara Reporters ta ruwaito.

An tattaro cewa wannan abu ya faru ne a Challenge junction.

Wani mazaunin garin, Kazeem Adeniyi, ya bayyanawa manema labarai a Ibadan ranar Talata cewa ginin titin da akeyi a hanyar yayi sababin hadarin.

A cewarsa, motoci sun saba bin barauniyar hanya, kuma hakan na janyo hadura.

Hakazalika ya tuhumi gudun da direbobi ke yi.

Wani mazaunin garin, Adekunle Lawa;. wanda aka fi sani da Saki First, ya yi Alla-wadai da yan kwantiragin da aka baiwa ginin hanyar.


Ya ce rashin kammala aikin ne ke haddasa hadura a hanyar.

Yace: "Jiya, Litinin, 11 ga Junairu, 2021, misalin karfe 10 na dare, wani hadari ya auku a Challenge junction inda akayi asaran ran wani yaro, Ayuba Raji, wanda kanin wata shahrarriyar mawakiya, Monsurat Raji, ne."

"Yaron na tuka babur ne yayinda mota mai dauke da shanu ta bugeshi."

"Sai matasa suka kona motar. Sai daga baya Saki First (Lawal) ya samu tuntubar yan sanda don su dakatad da lalacin da matasan ke yi."

"Muna jajantawa iyalan mamacin; wajibi ne masu kwangila suyi wani abu kan hanyan."

Source: legit


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/J9zhUeQqg52KIxyFnYByJN

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN