Yadda yansanda suka kashe mahaifiya da jaririnta garin tseren kama Yan Yahoo


Wata mahaifiya tare da Jaririn da take goye da shi a cikin Keke napep sun mutu bayan motar Hilux na yansanda ta ci karo da Keke napep da suke ciki sakamakon haka matar da jaririnta suka mutu nan take a Birnin Warri na jihar Delta.

Shafin ISYAKU.COM ya samo cewa ana zargin cewa wasu yansandan ofishin yansanda na Ebrumede ne suka biyo wasu samari a guje da motarsu kirar Hilux da niyyar kamasu bayan sun yi zargin cewa yaran yan Yahoo ne.

Garin tsananin gudu don ganin sun kama samarin, sai motar Hilux da yansandan ke ciki ta ci karo da Keke napep da matar ke ciki goye da jaririnta, lamari da ya sa Keke napep ya ruguje kuma matar da jaririnta suka mutu nan take.

Ganin haka ke da wuya,, sai yansanda suka yi kokarin tserewa, amma matasa suka hana su zuwa ko ina, kuma suka banka wa motar yansanda wuta ta kone kurmus.

Sai dai kawo yanzu ba wani bayani kan ko me ya faru da yansandan.


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/LKeYYgwzLbW8DdHbjNuEos

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN