Wasu yan bindiga a jihar Kogi sun kwashe matafiya yan kasuwa daga jihar Kano wadanda ke hanyarsu ta zuwa jihar Abia, kudu maso gabashin Najeriya.
Yan kasuwan, dukkansu yan Kantin Kwari, na hanyar tafiya Aba ne a jihar Abia domin siyayyarsu yayinda yan bindiga suka far musu kuma suka shiga da su cikin daji, Daily Trust ta ruwaito.
Dirakta manajan kasuwar Kantin Kwari, Alhaji Abba Bello, ya tabbatar da hakan.
A cewarsa, "Mutanen da aka sace su 18 ne, amma kawo yanzu mun samu sunayen 12, amma muna kyautata zaton su 18 ne."
"Suna kan hanyar tafiya Aba a Abiya yayinda yan bindiga suka taresu a hanyar Lokoja-Okene a jihar Kogi."
Alhaji Bello ya ce har yanzu bai samu labari ko yan bindigan sun tuntubi iyalan wadanda aka sace don bukatan kudin fansa ba.
Amma wasu majiyoyi sun bayyana cewa masu garkuwa da mutanen sun bukaci milyan 50 amma daga baya suka amince da karban milyan 27.
Source: legit
https://chat.whatsapp.com/
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari