Rahoton jaridar hausa.legit.ng sun nuna cewa Muhammad Tambari Yabo, mataimakin sufeto-janar na yan sanda mai ritaya, ya mutu.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa ya mutu a asibitin koyarwa na jami’ar Usman Danfodiyo, jihar Sokoto a ranar Asabar, 9 ga watan Janairu, bayan yar gajeriyar rashin lafiya.
Koda dai ba a bayyana musababbin ciwonsa ba, Legit.ng ta lura cewa babban jami’in dan sandan mai ritaya ya mutu ne a daidai lokacin da ake sake samun hauhawan wadanda suka mutu sakamakon annobar korona.
An gudanar da jana’izar marigayin da misalin karfe 2.30 na rana, a garin Yabo na Karamar Hukumar Yabo da ke Jihar Sokoto.
Gabanin ya kai mukamin Mataimakin Babban Sufeton ’Yan Sanda wato AIG, ya rike mukamin Kwamishinan ’Yan Sanda a Kaduna, Kano da Jihar Legas har sau biyu da kuma Oyo da Zamfara da Imo jaridar Aminiya ta ruwaito.
https://chat.whatsapp.com/
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari