Jam'iyyar APC na harin samun sababbin mambobi miliyan 2 a Adamawa


Jam’iyyar APC ta ce tana shirin yin rajistar mambobi miliyan 2 a Adamawa a ci gaba da rajistar membobin da ke gudana a duk fadin kasar, Vanguard ta ruwaito.

Farfesa Tahir Mamman, memba Mai Kula da Kwamitin Shirye-shiryen Babban Taro na APC ya fadi haka ne a wani taron manema labarai ranar Asabar a Yola.

“Muna so mu ga akalla mazauna Adamawa miliyan biyu a matsayin mambobi masu rajista na jam'iyyar APC a cikin rajistar membobin da ke gudana.

"Da yardar Allah a 2023, zai zama APC 'SAK' a dukkan matakan Tarayya, Jiha har zuwa Kananan Hukumomi (LGAs)," in ji shi.

Mamman ya ce tun farko jam'iyyar ta shirya Mega Rally a jihar don karbar wasu fitattun mutane da suka sauya sheka daga wasu jam'iyyun, amma dole ta fasa taron saboda cutar COVID-19.

Shima da yake jawabi, Sanata Isiyaku Abbo, mai wakiltar Yola ta Arewa, wanda ya sauya sheka daga PDP zuwa APC ya ce sauya sheka da yayi don bukatun mutane ne, yana mai cewa bai fita domin ya yanke kauna ba ne.

Abo ya bukaci hukumomin tsaro a jihar da su nisanta kansu da siyasa yayin gudanar da ayyukansu don tabbatar da adalci.

Mista Ibrahim Bilal, shugaban jam'iyyar APC na jihar, ya bukaci magoya bayan jam'iyyar da masu biyayya da su tabbatar sun yi rajista a mazabunsu a duk fadin jihar don tabbatar da nasarar aikin

A wani labarin, Wata babbar kotun tarayya dake zaune a Abuja ta yi watsi da karar amfani da kwalin jabu da jami'yyar All Progressives Congress APC ta shigar kan gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki.

Alkali Ahmed Mohammed ya yi watsi da karar nan ranar Asabar, Channels TV ta ruwaito.

APC da wani jigon APC Edobor, sun shigar da karan cewa gwamna Obaseki ya yi amfani da takardan bogi yayinda yake neman takaran gwamnan jihar da akayi ranar 19 ga Satumba, 2020.

Source: legit


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/J9zhUeQqg52KIxyFnYByJN

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN