Shekaru 5 ina sayarwa mutane mushen kaji a Maiduguri, Ebere


Wani mutum mai suna, Hassan Ebere, ya bayyana yadda ya sayar da mushen kaji sama da 6,000 ga al'ummar Maiduguri tsawon shekaru biyar yanzu domin neman kudin ciyar da kansa.

Ebere ya bayyana hakan ne yayin magana da kamfanin dillancin labarai (NAN), bayan jami'an NSCDC suka damkeshi ranar Laraba a jihar Borno.


"Na kan je rafin Ngadabul, bayan gidan talabijin BRTV, inda nike daukan mushen kajin da gidajen gona suka jefar, " ya bayyana.

"Kowani mako, na kan dauki guda goma ko fiye da haka, sannan in gyara kuma in sayarwa mutane.
"

"Kasuwannin da nake sayarwa sune kasuwar Kifin Baga, kasuwar Monday Market, shagunan masu Suya, da gidajen abinci, a cikin gari."

"N700 zuwa N800 nike sayarwa. Amma idan suka kai yan kwanaki (ban sayar ba), na kan kai gidajen giya a bayan Ngomari in sayar da su N250," ya kara.


Ebere ya ce shaidan ne ya tura shi aikata wannan abu kuma yana rokon a yafe masa.

Shugaban hukumar NSCDC na jihar Borno, Abdullahi Ibrahim, ya ce an damke mutumin ne yayinda yake gyaran kajin a bayan gidan talabijin da rediyo na BRTV ranar 2 ga Junairu, 2021

Source: legitLatsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/J9zhUeQqg52KIxyFnYByJN

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN