Mai koyon tukin mota ya kashe yara 6 da Marsandi da yake tukawa


Wata mota kirar Marsandi (Mercedes) wacce ke dauke da alamar mai koyon tuki, ta bi ta kan wasu yara guda shida kuma ta murkushe su har lahira nan tàke.

Lamarin ya faru ne ranar 16 ga watan Janairu a garin Arue-Uromi, da ke karamar hukumar Esan-North East  a jihar Edo.


Isyaku.com ya sàmo cewa motar ta yi kokarin kauce wa rami ne, sai ta kwace wa direban da ke koyon tuki ta bi ta kan yaran guda shida da suke buga kwallon kafa kuma ta kashe su nan take.

Daga bisani fusatattun matasa sun banka wa motar wuta ta kone kurmus.


Kwamandan FRSC na jihar Edo Henry Benamaisia ya tabbatar da faruwar lamarin a wata takarda da ta fito daga ofishinsa kan lamarin ga manema labarai.


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/LKeYYgwzLbW8DdHbjNuEos

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Previous Post Next Post

Information


Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/EsSeIwnS18mKkhQwHP3mFx

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari