Gwamnan Ondo ya ba makiyaya sati daya su fice daga dajin jiharsa


Legit.ng Hausa ta fahimci cewa gwamnan Ondo, Rotimi Akeredolu, ya bada wa’adin mako daya ga makiyaya su bar kungurumin jejin da ke cikin jiharsa.

Mai girma gwamnan Ondo ya bada wannan wa’adi ne a yankurin da yake yi na kawo karshen matsalar garkuwa da mutane da sauran ta’adin da ake yi a jihar.

Sanarwar Rotimi Akeredolu ta fito ne kai tsaye a shafinsa na Twitter, a ranar Litinin 18 ga watan Junairu. 2021.

Rotimi Akeredolu a jawabin na sa yake cewa an maida jejin jihar Ondo wuraren tafka ta’adi, don haka a matsayinsa na gwamna ya dauki wannan mataki a yau.

Yace: “A yau, mun dauki babban mataki na kawo karshen matsalar garkuwa da mutane, da sauran danyen ayyukan da ake yi da muka samu labari a rahotonmu.

“Ana alakanta wadannan munanan abubuwa da wasu miyagu da ke fakewa da sunan makiyaya.” Inji gwamnan.

“Wadannan miyagu sun maida jejinmu wuraren ajiye wadanda suka yi garkuwa da su, suna tattauna yadda zasu karbi kudin fansa da yin sauran laifuffuka.”


Daga cikin matakan da aka dauka, za a bar duk wasu jeji nan da kwana bakwai. An kuma haramta kiwo da dare, sannan an hana dabbobi yawo a manyan tituna.

Gwamna ya kuma hana kananan yara kiwo, sannan bayan wannan wa’adin ya cika, gwamnati za ta bada damar duk mai bukatar yin kiwo, ya yi rajista da hukuma.

A yau ne kuma muke samun labari cewa hedikwatar tsaro cewa ‘yan bindigan da ke ta’adi a Zamfara, sun gane ba su da wayau a hannun dakarun sojojin kasa.

Janar John Enenche ya ce dakarun Sojoji sun yi wa ‘Yan bindiga rugu-rugu a dajin Zamfara.

Sojojin Najeriya na Operation Hadarin Daji sun kashe tsageru 35 a dajin yankunan Bungudu da Muradun a jihar Zamfara, har sun karbe wasu dabbobi da aka sace.

Source: 


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/LKeYYgwzLbW8DdHbjNuEos

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN