An sami tashin hankali a kasuwar garin Ribah na karamar hukumar Danko-Wasagu da ke Masarautar Zuru a kudancin jihar Kebbi da yammacin ranar Litinin 25/1/2021 bayan wasu mutane sun dira kasuwar Ribah da misalin karfe 5:00 na yamma suka dinga dukan jama'a da makamai.
Wannan lamarin ya haifar da rudani tare da fargaba tsakanin jama'a da ke cikin kasuwar, sakamakon haka jama'a suka dinga gudu ko ta ina a cikin kasuwar wacce take ci ranar Litinin na kowane mako.
Ana zargin cewa an kashe mutum daya a wannan hargitsi, an kuma raunata mutane da dama.
Masarautar Zuru ta fada cikin tsananin matsalar rashin tsaro daga baya bayannan sakamakon farmakin yan bindiga da rikicin cikin gida na wasu mutane masu dauke da makamai.
Lamari da ya haifar da kashe kashen rayukan bayin Allah, musamman a yankin Bena da ta yi iyaka da jihar Zamfara.
DAGA ISYAKU.COM
https://chat.whatsapp.com/LKeYYgwzLbW8DdHbjNuEos
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari